ha_tn/mat/18/10.md

979 B

Ku kula fa

"Ku yi hankali" ko kuma "Ku tabbatar cewa"

kada ku rena kananan nan

"kada ku ɗauki waɗannan kananan da rashin muhimmanci." AT: "ku ba waɗannan kananan nan girma"

Domin ina gaya maku

Wannan na ƙara nanata maganar Yesu da ke biyo baya ne.

mala'ikunsu a koyaushe na duban fuskar Ubana da ke sama

Malaman Yahudawa suna kayar da cewa mala'iku mafi muhimmanci ne kawai suna iya kasancewa a gaban Allah. Yesu kuma yana nufin cewa mala'iku mafi muhimmanci suna magana da Allah akan waɗannan kananan nan. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

a koyaushe na duban fuskar Ubana

Wannan wata karain magana ne da ke nufin cewa suna gaban Allah. AT: "suna kusa da Ubana a kodayaushe" ko kuma "suna gaban Ubana a kodayaushe" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Ubana

Wannan wata lakaɓi ne mai muhimmanci da ke bayyana ɗangartakan da ke tsakanin Allah da Yesu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)