# Ku kula fa "Ku yi hankali" ko kuma "Ku tabbatar cewa" # kada ku rena kananan nan "kada ku ɗauki waɗannan kananan da rashin muhimmanci." AT: "ku ba waɗannan kananan nan girma" # Domin ina gaya maku Wannan na ƙara nanata maganar Yesu da ke biyo baya ne. # mala'ikunsu a koyaushe na duban fuskar Ubana da ke sama Malaman Yahudawa suna kayar da cewa mala'iku mafi muhimmanci ne kawai suna iya kasancewa a gaban Allah. Yesu kuma yana nufin cewa mala'iku mafi muhimmanci suna magana da Allah akan waɗannan kananan nan. (Dubi: [[rc://*/ta/man/translate/figs-explicit]]) # a koyaushe na duban fuskar Ubana Wannan wata karain magana ne da ke nufin cewa suna gaban Allah. AT: "suna kusa da Ubana a kodayaushe" ko kuma "suna gaban Ubana a kodayaushe" (Dubi: [[rc://*/ta/man/translate/figs-idiom]]) # Ubana Wannan wata lakaɓi ne mai muhimmanci da ke bayyana ɗangartakan da ke tsakanin Allah da Yesu. (Dubi: [[rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples]])