1.3 KiB
Mahaɗin Zance:
Bayan aukuwar haɗarin jirgin ruwar, Jama'ar da ke tsibirin Malita sun taimaka wa Bulus da kowa da kowa da ke jirgin. Suka yi zama a wurin har na wata 3.
Muhimmin Bayani
A nan kalmar nan "mu" na nufin Bulus, marubucin, da kuma waɗanda suake tafiya tare da su, ammam ba masu karatu ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-exclusive)
Sa'adda muka sauka lafiya
AT: "Sa'adda muka iso lafiya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)
sai muka ji
Bulus da Luka suka ji sunan tsibirin. AT: "muka ji daga baƙin mutanen" ko kuma "muka ji daga mazaunan wurin" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-exclusive)
cewa sunan tsibirin Malita
Malita wata tsibiri ce da ke kudancin tsibirin Sicily a yau. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)
Mutanen garin
"Ainihin 'yan wurin"
sun nuna mana alheri matuka
Ana maganar alheri kamar wani abu ne musamman da ake iya nunawa. AT: "ba ƙaramin alheri suka nuna mana ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)
nuna mana alheri matuka
"nuna mana baban alheri matuka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-litotes)
don sun hura wuta
"sun haɗa ƙirare da su reshe suka ƙone su"
suka marabce mu dukka
Wannan na iya nufin 1) "suka marabci dukkan mutanen da ke jirgin ruwan" ko kuma 2) "suka marabci Bulus da dukkan abokan tafiyansa."