1.6 KiB
ta gabato, tana gabatowa da sauri
Maimaicin kalmar "gabato", tare da furcin "gabatowa da sauri" suna jaddada cewa ranar da Yahweh zai hukunta mutanen tana dab da abkuwa. AT: "tana kusa, kuma za ta iso nan ba da jimawa ba".
rana ta hasala ce ... ranar hallakarwa
Wannan furcin yana jaddada yadda munin hukuncin Allah zai kasance. Kalmomin da aka mora suna tare domin nuna yanayin hallakarwa na wannan hukuncin karshe da Allah zai yi. Suna jaddada al'amarin.
Ranar azaba da wahala
Kalmomin "azaba" da "wahala" suna da ma'ana kusan daya, kuma suna jaddada tsananin wahalar mutanen. AT: "ranar da mutane za su sha mumunar azaba".
ranar tsawa da hallakarwa
A nan, "tsawa" tana nufin hukuncin Allah. Kalmar "hallakarwa" tana bayyana munin wannan hukuncin.
ranar duhu, baki kirin
Kalmomin "duhu" da "baki kirin" suna da ma'ana kusan iri daya, kuma suna jaddada tsananin duhun. Duka kalmomin suna nuni ne da lokacin masifa ko hukuncin Allah. AT: "ranar da ke cike da duhu" ko "ranar hukunci mai bantsoro".
ranar gizagizai da bakin duhu
wannan furcin yana da ma'ana iri daya da maganar da ta gabata, kuma yana jaddada ra'ayi daya. Kamar wancan furcin, "gizagizai" da "bakin duhu" suna nuni da hukuncin Allah. AT: "rana mai cike da gizagizai masu duhu da tsawa".
ranar busa kaho da yin kururuwar yaki
Kalmomin "kaho" da "kururuwar yaki" suna da ma'ana kusan iri daya a nan. Duk biyun hanyoyin kiran mayaka ne su shirya don yaki. AT: "ranar da mutane za su yi kururuwar yaki".
birane masu garu da hasumiya masu tsawo
Wadannan kalamai biyu suna nufin wuraren tsaro na mayaka. AT: "birane masu kakkarfar garkuwa".