1.5 KiB
Muhimmin Bayyani:
Wannan itace farkon labarin da ya maimaiye littafin Matta [18:35] inda Yesu yake koyarwa game da rayuwa a cikin mulkin sama. Anan, Yesu yana amfani ne da karamin Yaro a koyaswan shi ga almajiran.
''Wanene mafi girma
"Wanene mafi muhimmanci" ko kuma "Wanene a cikinmu mafi muhimmanci"
a mulkin sama
Jimlar nan "mulkin ssama" na nufin sarautar Allah a matsayinsa na sarki. An yi amfani da wannan jimlar a littafin Matta ne kadai. In ya yiwu, ku bar "sama" a naku juyin. AT: "a mulkin Allah" ko kuma "yayin da Allahn mu na sama zai kafa mulkinsa a duniya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)
Hakika ina gaya maku
"Ina gaya maku gaskiya." Wannan na kara nanata magan Yesu da ke biya baya ne.
idan baku juya ... kanana yara ba, babu yadda zaku shiga
AT: "sai kun canza ... kananan yara kamun ku shiga" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublenegatives)
zama kamar kananan yara
Yesu yana amfani ne da wannan karin magana ya koya wa almajiransa cewa kada su damu da zancen wanene mafi muhimmanci. Sai dai su damu da zancen wanene ke kaskatar da kansa kamar karamin yaro. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)
shiga mulkin sama
Jimlar nan "mulkin sama" na nufin sarautar Allah a matsayin sa na sarki. An yi amfani da wannan jimlar a littafin Matta ne kadai. In ya yiwu, ku bar "sama" a naku juyin. AT: "shiga mulkin Allah" ko kuma "zama da Allahn mu a sama yayin da ya kafa mulkinsa a nan duniya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy )