ha_tn/mat/01/01.md

1.3 KiB

Muhimmin Bayyani:

Marubucin ya fara da asalin Yesu domin ya nuna cewa Yesu daga zuriyar Sarki Dauda ne da kuma na Ibrahim. An cigaba da asalin har zuwa 1:1-17 .

Littafin asalin Yesu Almasihu

Za a iya fassara wannan kamar cikakken zance. AT: "Wannan ita ce jerin sunayen kakanin Yesu Almasihu"

Yesu Almasihu, ɗan Dauda, ɗan Ibrahim

Akwai zuriya da yawa tsakanin Yesu, Dauda, da Ibrahim. Anan "ɗa" na nufin "ɗan zuriya". AT: "Yesu Almasihu, zuriyar Dauda, wanda shi zuriyar Ibrahim ne"

Ɗan Dauda

A wani lokacin ana amfani da kalmar "ɗan Dauda" kamar laƙani, amma a nan kamar ana amfani da shi a gano zuriyar Yesu.

Ibrahim shine mahaifin Ishaku

Akwai hanyoyi dabam dabam da za a iya fassara wannan. A yadda ka fara fassara anan sai a ci gaba har karshen jerin sunayen kakanin Yesu. AT: "Ishaku ɗan Ibrahim"

Ishaku mahaifin ... Yakubu mahaifin

A nan an riga an fahimci kalmar "shine". AT: "Ishaku shine mahaifin ... Yakubu shine mahaifin" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-ellipsis)

Feresa ...Zera ...Hasruna ...Aram

Wadannan sunayen maza ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

Feresa mahaifin ... Hasruna mahaifin ...

A nan an riga an fahimci kalmar "shine". AT: "Feresa shine mahaifin ... Hesruna shine mahaifin" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-ellipsis)