ha_tn/job/28/12.md

1.6 KiB

Muhimmin Bayani:

A cikin Ayuba 28: 12-28, ana magana da hikima da haziƙanci kamar dai su abubuwa ne masu tamani waɗanda suke wani wuri kuma mutane suna son neme su. Neman hikima da haziƙanci yana wakiltar zama mai hikima da koyon fahimtar abubuwa da kyau. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Daga ina za a samo hikima? Ina ne wurin haziƙanci?

Waɗannan tambayoyin suna ma'ana dai-dai kuma suna amfani dasu don nuna cewa yana da matukar wahala a sami hikima da haziƙanci. AT: "Yana da matukar wahala a sami hikima da haziƙanci." (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]])

Mutum bai san darajarta ba

Ma'anar mai yiwuwa ita ce 1) ana magana da hikima kamar dai wani abu ne da mutane zasu iya siye. AT: "Mutane ba su san abin da ya dace ba" ko 2) kalmar da aka fassara da "farashi" ma'ana "wuri." AT: "Mutane ba su san inda yake ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ko a samo ta a ƙasar masu rai

"kuma ba a samo shi a ƙasar masu rai ba." “a ƙasar masu rai” tana nufin wannan duniyar da mutane suke zama. Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai aiki. AT: "kuma ba wanda zai iya samun hikima a duniyar nan" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Zurfafan ruwaye a ƙarƙashin ƙasa sun ce, 'Bata cikina,' teku ta faɗa, 'Bata tare da ni

An gabatar da ruwa mai zurfi da teku kamar dai mutane ne da zasu iya magana. AT: "Hikima ba ta cikin zurfafa cikin ruwa a karkashin ƙasa, ba kuma cikin teku" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)