ha_tn/act/17/16.md

722 B

ya yi fushi a ransa, da ya ga birnin cike da gumakai

A nan "ransa" na nufin Bulus da kansa. AT: "hankalinsa ya tashi domin ya ga cewa garin yana cike da gumakai ko ta ina" ko kuma "ganin gumakai a ko ina a garin ya tayar masa da hankali" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

Ya tattauna

ya yi muhawwara" ko kuma "ya yi shawara" Wato akwai hulda da masu sauraro, ba wai Bulus yana ta jawabi shi kaɗai ba. Su ma suna magana da shi.

da masu yin sujada ga Allah

Wato Al'ummai (wanda ba Yahudawa ba) da ke Yabon Allah suna kuma bin sa, amma ba su kiyaye duka dokokin Yahudawa.

a kasuwa

"a cikin taron jama'a." Wurin harkokin siya da sayarwa.