ha_tn/act/15/27.md

986 B

su gaya maku waɗannan abubuwa da kansu a kuma na su kalamu

Wannan jimlar na nanata cewa Yahuza da Sila za su faɗi abu ɗaya da manzanni da dattawa sun rubuta. AT: "wanda da kansu za su yi maku magana game da abubuwan da muka rubuta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

kada mu sa maku nauyi fiye da waɗannan abubuwan

Wannan na maganar dokokin da mutane ke buƙatar kiyaye wa ne kamar sun zama wasu kayayyaki e=ne da mutane za su ɗaɗɗauka a bisa kafaɗansu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

wa gumaka hadaya

Wannan na nufin cewa ba yarda su ci naman wata dabba da wani ya miƙa wa gumaka hadaya ba.

jini

Wannan na nufin shan jini ko cin naman da ba a janye jinin sa ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

abubuwan da aka musƙure

Dabba da aka musƙure ya mutu, amma ba janye jinin sa ba.

Ku huta lafiya

Wannan na sanar da ƙarshen wasikar. AT: "Wassalam" ko kuma "Ku zamna lafiya" ko kuma "Allah ya bishe ku"