ha_tn/2th/02/05.md

766 B

Baku tuna ba ... waɗannan abubuwa?

Bulus ya yi amfani da tambayar da ba lallai ne a bada amsa ba don ya tunashe su game da koyarwarsa a lokacin da ya ke tare da su a dã. Ana iya bayyana wannan cikin furci. AT: "Na tabbata kun tuna ... waɗannan abubuwan." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

waɗannan abubuwa

Wannan na nufin dawowar Yesu, ranar Ubangiji, da mutum mai aikata mugunta.

zai bayyanu a lokacin da ke daidai

AT: "Allah zai bayyana mutum mai aikata mugunta a sa'ad da lokacin ya yi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

asirin tãke shari'a

Wannan na nufin asirin mai tsarki da Allah ne kaɗai ya sani.

wanda ke tsaida shi

a tsaida wani ita ce a riƙe su ko kuwa a hana su yi abin da suna so su yi.